Ma’aikatar kula da sufuri ta kasar Sin ta sanar a yau Litinin cewa, ta dakatar da karbar kudi na musammam a tashoshinta na ruwa ga jiragen da kamfanonin Amurka ko daidaikun mutane ko hukumomin kasar suka mallaka ko suke tafiyar da harkokinsu.
Wannan dakatarwa ta tsawon shekara 1, ta fara aiki ne daga karfe 1:01 na rana, a yau Litinin.
Haka kuma, ma’aikatar ta sanar da dakatarwa ta tsawon shekara 1 kan bincike yadda bincike na sashe na 301 na Amurka ya yi tasiri kan tsaro da muradun raya harkokin zirga zirgar jiragen ruwan Sin da bangaren kera jiragen da ma kan tsarin ayyukan masana’antu da na samar da kayayyaki da suka shafi banagren.
A cewar ma’aikatar, wadannan matakai sun yi daidai da matsayar da aka cimma yayin tattaunawa ta bayan bayan nan da aka yi tsakanin Sin da Amurka kan tattalin arziki da cinikayya a birnin Kuala Lumpur na Malaysia.
Bugu da kari, ma’aikatar ta sanar da dakatarwa ta tsawon shekara 1, na aiwatar da matakan ramuwa kan wasu kamfanoni 5 dake karkashin kamfanin Hanwha Ocean na Korea ta Kudu, mai kera jiragen ruwa, wadanda ke da alaka da Amurka. (Mai fassara: FMM)














