Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana a ranar Alhamis cewa, kasar Sin na adawa da kuma Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa shugaban kungiyar Hamas Ismail Haniyeh, kuma ta damu matuka cewa lamarin na iya jefa yankin cikin babban rudani.
Kakakin ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai na yau da kullun, lokacin da aka bukaci ya yi tsokaci kan tasirin kisan Haniyeh ga kokarin samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, da kuma yarjejeniyar Beijing da aka rattaba hannu a kai da kasar Sin ta shiga tsakani kwanan nan.
Lin ya ce bai kamata a kara ruruta wutar rikici ba, ya kuma yi kira ga cikakken tsagaita bude wuta kuma na dindindin a Gaza cikin gaggawa.
Ya kara da cewa, kasar Sin tana goyon bayan sulhun cikin gida na Falasdinawa, kuma ta yi imanin cewa, wannan muhimmin mataki ne na warware batun Falasdinu, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.
Lin ya kara da cewa, kasar Sin ta yabawa bangarorin Falasdinawa bisa kokarin da suka yi kan yarjejeniyar da aka cimma a birnin Beijing, kuma tana fatan ganin ranar da bangarorin Falasdinawa za su sansanta, kuma a kan haka za su samu ‘yantacciyar kasa da wuri-wuri. Kuma kasar Sin za ta yi aiki da bangarorin da suka dace don cimma wannan manufa. (Yahaya)