Sarkin Kano na 16 Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga jama’a da kada su bari a yi amfani da su wajen lalata Kano da Arewa da kasa baki daya.
Sarkin ya yi magana ne yayin da masu zanga-zangar suka koma kan tituna duk da dokar hana fita da aka sanya biyo bayan tashe-tashen hankula.
- Zanga-zanga: Kada Ku Mayar Da Kano Da Arewa Baya – Sanusi II
- Sin Ta Damu Kisan Shugaban Hamas Zai Iya Haifar Da Babban Tashin Hankali A Gabas Ta Tsakiya
Leadership ruwaito yadda masu zanga-zangar suka sake haduwa a yankin Tudun Wada na karamar hukumar Nassarawa da ke Kano, da yammacin ranar Juma’a.
Sun sake haduwa ne bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sassauta dokar hana fita don bai wa jama’a damar zuwa Masallacin Juma’a.
A wani taron manema labarai da aka gudanar a fadarsa ta Gidan Rumfa a yammacin ranar Juma’a, Sarkin ya nuna matukar damuwa kan yadda aka wawashe kadarorin jama’a tare da lalata wasu sakamakon zanga-zangar.
Sarkin ya ce abin da ya faru koma baya ne ga jihar, yankin Arewa da ma kasa baki daya.