Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da wata shawara da aka yanke game da daukar matakan martani a kan wasu kamfanonin sarrafa makamai na Amurka guda 7 da kuma wasu jami’ai masu nasaba da hakan, a yau Juma’a.
A yayin gudanar da taron manema labarai na kulli yaumin da aka gabatar yau, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ta Sin, Mao Ning, ta bayyana cewa, kasar Sin ta dauki matakin hakan ne bayan Amurka ta sanar da wani sabon tallafin soji da sayar da makamai ga yankin Taiwan na kasar Sin a kwanan baya, da kuma kafa dokar bayar da izinin karfafa tsaron kasa mai lakabin NDAA ta shekarar kasafin kudi ta 2025 da ta kunshi takunkumai na mugunta a kan kasar Sin.
Dangane da batun wasu kasashe da suka zama ‘yan amshin shata suka tsunduma cikin yaudarar siyasa da sunan wai kare hakkin dan Adam kuwa, Mao Ning ta ce Canada ta kakaba takunkumi ga wasu jami’an kasar Sin da nufin fakaicewa da guzuma a harbi karsana saboda wai tauye ‘yancin bil’adama, amma kuma kasar Sin ba za ta rungume hannu ta zuba ido ba, don kuwa ta dauki matakan martani daidai da tanadin doka wanda gaba daya ba su kauce hanya ba kuma suka yi daidai a ma’aunin hankali. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)