A yau Laraba, kasar Sin ta fitar da jerin kamfanoni 500 mafiya karfi na shekarar bana, adadin da ya kunshi kamfanoni 264 da suka yi fice a fannin kere-kere, wanda kuma ya shaida karuwar kamfanoni 8 a fannin, kan wadanda suka shiga jerin a bara, tare da ci gaba da bunkasar fannin cikin shekaru 3 a jere.
Kungiyar kamfanonin kasar Sin, da hukumar lura da kamfanonin kasar ne suka wallafa jerin sunayen kamfanonin da suka yi fice, yayin taron da suka gudanar a birnin Hefei, na lardin Anhui dake gabashin kasar Sin.
Sai kamfanonin da ke da adadin kudaden shiga da suka kai yuan biliyan 46.998, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 6.55 ne ke shiga jerin manyan kamfanoni 500 na kasar Sin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp