Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da wani rahoto kan take hakkin dan Adam a Amurka a shekarar 2024 yau Lahadi.
Rahoton ya ce, a Amurka, kalaman wariyar launin fata na ci gaba da yaduwa kamar wutar daji, inda ake ci gaba da nuna kyama da wariya ga kananan kabilu. Kazalika, a Amurka, Amurkawa da suke ‘yan asalin Afirka sun fi fuskantar harbin kisa da bindiga daga ‘yan sanda har sau uku fiye da fararen Amurkawa.
Har ila yau, a cikin dukkan yaran da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai ba tare da sakin talala ko yi musu afuwa ba, kashi 61 cikin dari yaran bakar fata ce. Yayin da aka amince tare da ba da kariya ga ma’aikatan hukumar shige da fice wajen mayar da wuraren tsare mutane su zama “kurkukun bakar fata” inda a nan ma azabtarwa ta kazanta. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp