Majalissar gudanarwar kasar Sin ta fitar da takardar bayani, game da bunkasa ci gaban mata mai taken “Nasarorin Sin a fannin bunkasa ci gaban mata a dukkanin fannoni a sabon zamani”.
Takardar bayanin da aka fitar a Juma’ar nan, na zuwa ne gabanin bude babban taron shugabanni na kasa da kasa na 2025, game da daidaiton jinsi, da karfafar rayuwar mata da zai gudana a nan birnin Beijing.
Takardar ta kunshi cikakkun bayanai na gabatar da falsafar kasar Sin, da ka’idoji da ayyukan kirkire-kirkire masu nasaba da ingiza daidaiton jinsi, da bunkasa rayuwar mata a dukkanin fannoni a sabon zamani.
Kazalika, ta fayyace muhimman nasarorin da matan kasar suka cimma, da tarin gudummawar da suka bayar, da jaddada himmar Sin wajen shiga a dama da ita a ayyukan hadin gwiwa na kasa da kasa masu nasaba da bunkasa rayuwar mata. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp