Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da wata takardar matsayar da gwamnati ta cimma a yau Laraba game da batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya da Amurka, inda ta jaddada muhimmancin yin shawarwari tsakanin bangarorin biyu bisa mutunta juna da hadin gwiwar samun nasara ga kowane bangare.
Takardar mai taken “Matsayin kasar Sin kan wasu batutuwan da suka shafi alakokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka” ta jaddada cewa, dangantakar tattalin arziki da kasuwancin Sin da Amurka na da matukar muhimmanci ba ga kasashen biyu kadai ba, har ma da kwanciyar hankali da ci gaban tattalin arzikin duniya.
- Amurka Ta Ƙara Wa Kayayyakin China Haraji Zuwa Kashi 104
- Babu Kuɗin Fansar Da Aka Biya Wajen Ceto Janar Tsiga – DHQ
Sai dai kuma, a ‘yan shekarun nan ana samun karuwar tarnaki ga hadin gwiwar kasashen biyu, musamman saboda karuwar manufofin mamaye komai da kariyar ciniki na Amurka.
Wadda aka tsara a cikin babi shida, takardar matsayar ta gwamnati ta sake tabbatar da yanayin moriyar juna ta cinikayya tsakanin Sin da Amurka.
Ta kara da bayyana cewa, kasar Sin ba ta neman cin bulus a harkar kasuwanci, kuma bangarorin biyu sun samu riba mai yawa daga hadin gwiwar tattalin arziki da suke yi. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp