Hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar da alkaluma a yau Litinin, wadanda ke cewa daga watan Jarairu zuwa Satumba na bana, yawan kudin cinikayyar shige da fice na kasar ya kai fiye da dalar tiriliyan 4.5, wanda ya karu da kashi 5.3% bisa na makamancin lokaci na bara.
Daga adadin, kudin cinikin shigo da kayayyaki ya kai fiye da dala tiriliyan 1.9, wanda ya karu da kashi 4.1%, yayin da adadin cinikin fitar da kayayyaki zuwa waje ya kai dalar tiriliyan 2.6, wanda ya karu da kashi 6.2%. (Amina Xu)