Tsarin mu’amalantar kasashen duniya na kasar Sin yana taka muhimmiyar rawa wajen zurfafa yin gyare-gyare da kuma ciyar da zamanantar da kasar gaba a wannan sabon zamani, hakan ya sanya take kiyaye muhimman ka’idoji, da samar da sabbin damammaki, da sa kaimi ga ci gaban bil Adam. Kana huldar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya na dauke da nufin wanzar da zaman lafiya a duniya, da sa kaimi ga samun bunkasuwa tare, da yin hadin gwiwa, da samun moriyar juna, da kawar da shakkun sauran kasashen duniya game da tsarinta na samun bunkasuwar duniya, da ba da gudummawa wajen yin mu’amalar wayewar kai. Kasar Sin ta sanya ruhi, karfi da dabi’unta nagartattu a yadda take mu’amalantar kasashen duniya, hakan ya sanya muryarta ke tasiri a dandalin duniya.
A cikin shekaru fiye da 100 da suka gabata, hada tushen tsarin Markisanci da hakikanin yanayi da al’adun gargajiya na kasar Sin, ya taimaka wa kasar wajen samun nasarori masu ban mamaki, da kuma taka muhimmiyar rawa wajen juyin juya halin tsarin gurguzu, da gine-gine da gyare-gyare. Tunanin Xi Jinping game da tsarin gurguzu tare da halayen kasar Sin a sabon zamani ya gabatar da sabbin ra’ayoyi, da sabbin tunani, da sabbin dabaru kan harkokin mulkin kasa. Wanda ya kunshi mafi kyawun al’adun Sinawa da kuma dabi’ar zamaninmu.
- Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Mataimakiyar Gwamna Ta Yi Kira A Guji Tarzoma A Rungumi Zaman Lafiya
- Yaushe Ne Za A Fitar Da Sama Tabeel Daga Fargaba
Ta hanyar inganta dabi’un bil Adama, tare da taimakawa wajen gina al’umma mai makomar bai daya ga bil Adama, da kuma sa kaimi ga bunkasa shirin raya kasa da kasa, da shirin samar da tsaro na duniya, da shirin wayewar kai, kasar Sin ta kara fahimtar da duniya cewa, wadannan ra’ayoyin sun bayyana halin da ake ciki game da ci gaba, da sa kaimi ga samun ci gaba na bai daya da kiyaye tsaro na duniya.
Mafi kyawun nasarorin da kasar Sin ta samu na ci gaba ya bayyana a cikin labaran gwagwarmaya na talakawar kasar, da kuma kyakkyawan yanayin da suke da shi na rayuwa. Shi ya sa kasar ke tabbatar wa al’ummomin kasa da kasa cewa, ita muhimmiyar mamba ce a cikin al’ummomin kasa da kasa, kuma ci gabanta yana da nasaba da ci gaban duniya, yayin da nasarorin da ta samu na ci gaba da bin tafarkin ci gaba na musamman, ke zama abin misali ga kasashe masu tasowa da ma masu ci gaba. (Mohammed Yahaya)