Babban bankin jama’ar kasar Sin da ma’aikatar kasuwanci da hukumar sa ido kan harkar hada-hadar kudi da hukumar kula da musanyar kudade ta kasar Sin, sun ba da wata hadaddiyar sanarwa kwanan baya mai taken “shawara game da aiwatar da gwajin manufar kara bude kofar Sin ga ketare bisa ma’aunin duniya a wasu yankunan ciniki cikin ’yanci dake da yanayin da ya dace a bangaren hada-hadar kudi”, inda aka gabatar da manufofi 20 daga bangarori 6, don gaggauta bude kofar Sin ga ketare a wadannan yankuna bisa wadannan manufofi.
Sanarwar ta ce, za a yi aikin gwaji a yankunan ciniki cikin ’yanci dake biranen Shanghai da Tianjin da Beijing da larduna Guangdong da Fujian da Hainan da sauransu, har ma da sauran dandalolin hadin gwiwa dake da muhimmin nauyin da kwamitin kolin JKS da majalisar dokokin kasar Sin suka dora a wuyansu a bangren kara bude kofa ga ketare, ta yadda za a tattara dabarun yayata wadannan manufofi masu zurfi ga bangarori masu yawa, don tabbatar da budewar kofar yankuna ko tasoshin ruwa masu ciniki cikin ’yanci bisa wadannan manufofi, da kuma la’akari da ci gaban da aka samu wajen yin kwaskwarima bisa tsarin da aka samar tare da nacewa a kan tabbatar da ingancin bunkasuwar tattalin arzikin Sin mai bude kofarta. (Amina Xu)