A yau Lahadi ne aka gabatar da sabon samfurin jirgin kasa kirar kasar Sin mai matukar sauri, wanda ka iya gudun kilomita 450 a duk sa’a, matakin dake nuni ga ci gaban da kasar ta samu a fannin samar da jirage masu matukar sauri da tsumin makamashi, da raguwar kara da ingancin birki.
An gabatar da jirgin sanfurin CR450 ne a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, kuma kamfanin sufurin jiragen kasa na Sin ko China Railway wanda ya kera shi, ya ce CR450 ya cimma nasarar kammala gwajin gudun kilomita 450 a sa’a daya, da madaidaicin gudun sufuri da ya kai kilomita 400 duk sa’a.
- Muhimman Abubuwan Da Suka Faru A Masana’antar Fina-finan Nijeriya A Shekarar 2024
- Maganin Zubewar Mama Da Yadda Ake Gyara Shi
Da zarar an fara sufurin fisinjoji da shi, ana sa ran jirgin zai rage tsayin lokacin tafiye-tafiye, da kara kyautata jin dadin matafiya. Kaza lika, duk da tsananin saurin jirgin, an tsara shi ta yadda zai samar da kariyar hadurra, da birki mai ingancin tsaiwa cikin sauri, da daidaiton sarrafawa.
Bugu da kari, an kara inganta bangaren tsumin makamashi, da kaso 22 bisa dari na turjiyar iska, da kaso 10 bisa dari na daukacin nauyin jirgin. Baya ga dadin tafiya ga matafiya, da raguwar kara ga wadanda ke cikinsa, an fadada kujerun zama da kaso 4 bisa dari.
An inganta na’urorin zamani na sarrafa jirgin kasan samfurin CR450, da damar tuntuba tsakanin na’urori da matuki, da tsarin lura da kare hadurra, da sauran hidimomi ga fasinjoji, wadanda ke nuni ga ci gaban fasahohin kirar jiragen kasa na Sin. (Saminu Alhassan)