Sojojin Nijeriya sun lalata haramtattun matatun guda 20 a yankin Niger Delta, yayin da suka kama mutane takwas da ake zargi da satar mai har lita 90,000.
Kakakin Sojojin Nijeriya runduna ta 6, Laftanar Kanal Danjuma Jonah Danjuma, ya bayyana a Fatakwal cewa wannan nasara ta biyo bayan farmaki daga ranar 23 zuwa 29 ga Disamba, 2024. Ya ce an kwato kwalekwale 21 da aka yi amfani da su wajen satar mai, da kuma mai da aka tace ba bisa ƙa’ida ba, ciki har da lita 37,000 da aka gano a Buguma da kewaye.
- Yadda Mai Haihuwar Fari Za Ta Kula Da Kanta (2)
- Halaye 8 Na Rayuwa Da Aka Fi So A Yi Shiru Maimakon Magana (2)
Haka zalika, sojojin sun lalata wuraren tace mai ba bisa ƙa’ida ba a yankunan Degema, da Omoku, da Odagwa, da kuma Imo River. A Bayelsa, an gano lita 8,000 na kayan sata, yayin da a Akwa Ibom aka kama lita 11,760 da ake shirin safararsu zuwa wata ƙasa.
Shugaban rundunar Sojojin bataliya ta 6, Manjo Janar Jamal Abdussalam, ya buƙaci jama’a da su ci gaba da bayar da bayanan sirri don kawo ƙarshen ayyukan masu satar mai a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp