Ofishin majalissar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da jerin tarukan ganawa da manema labarai game da “kammala ingantaccen tsarin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14 cikin nasara”.
Game da hakan, ministan sufuri na kasar Liu Wei ya ce cikakken tsarin raya kasa da ya game sassa uku na sufuri muhimmin jigo ne na bunkasa tattalin arziki, kana yana matukar tallafawa wajen gina sabon salon samar da ci gaba. Ya ce a halin da ake ciki, kasar Sin ta gina tsarin sufuri mafi girma a duniya a fannonin uku.
Bisa alkaluman da aka fitar, an kammala kaso 81.5 bisa dari na layukan dogon kasar na zirga-zirgar jiragen kasa masu matukar sauri tare da fara aiki da su, inda tsayin sufurin da ake iya yi a kan su ya kai kilomita 48,000, adadin da ya kai kaso sama da 70 bisa dari na jimillar wanda ake da shi a duniya baki daya, kana ya karade kusan kaso 97 bisa dari na daukacin biranen kasar masu adadin mutane da ya kai sama da 500,000.
Kazalika, an yi nasarar sada manyan hanyoyin mota 33 da juna, wadanda jimillar tsayinsu ya kai kilomita 191,000, sun kuma karade kaso 99 bisa dari na jimillar biranen kasar masu yawan jama’ar da ya haura 200,000.
A daya bangaren kuma, adadin manyan hanyoyin ruwa da aka samar ya kai kaso 70.4 bisa dari na jimillar mizanin da ake son aiwatarwa, kana ikon tasoshin ruwan kasar na sufurin jiragen ruwa ya kai matsayi mafi girma a duniya cikin shekaru da dama. Sai kuma sufurin sama da hidimominsa suka karade kaso 92.6 bisa dari na yankuna masu matsayin gundumomi, da kaso 91.2 bisa dari na daukacin al’ummun kasar ta Sin, yayin da a karkashin sashen aikewa da sakwanni, aka samar da cibiyoyin kasuwanci sama da 500,000 a fadin kasar. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp