A yau Talata ne kasar Sin ta yi nasarar harba sabbin taurarin dan’adam guda bakwai, ta amfani da rokar Long March-6C. An cimma nasarar harba taurarin ne da karfe 11:21 na safe agogon Beijing, daga cibiyar harba kumbuna ta Taiyuan dake lardin Shanxi na arewacin kasar, sun kuma shiga da’irar da aka tsara yadda ya kamata.
Wannan ne karo na 665, da aka yi amfani da samfurin rokar Long March domin gudanar da aikin harba taurarin dan’adam na kasar Sin, kamar dai yadda cibiyar ta tabbatar. (Saminu Alhassan)
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
ADVERTISEMENT