Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce ba zai janye shirinsa na samar da wani tsari da zai rage tsadar man fetur da sauƙaƙa wa ‘yan Nijeriya wahalar tsadar rayuwa ba.
Atiku, ya ce manufar shirinsa ita ce rage tasirin da cire tallafin man fetur ya jefa wa talakawa.
A cewar sanarwar da babban mai taimaka masa kan harkokin sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku na shirin tallafa wa matatun mai na cikin gida domin ƙara samar da man fetur a Nijeriya da rage kuɗin da ake kashewa wajen samar da shi.
Sanarwar ta ce idan aka samar da wani tallafi, za a ƙayyade adadinsa a zahiri, a saka shi cikin kasafin kuɗin gwamnati, sannan masu bincike masu zaman kansu su riƙa duba yadda ake kashe kuɗaɗen.
Atiku ya kuma musanta bayanan ‘yam adawa da ke cewa zai dawo da tallafin sannan ya sakw cire shi daga baya.
A cewarsa, babban burinsa shi ne rage tsadar rayuwa, rage kuɗin sufuri da samar da kayayyaki, tare da ƙara samar da man fetur a cikin gida.
Ya kuma soki manufofin tattalin arziƙin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa sauye-sauyen da aka yi sun ƙara wa ‘yan Nijeriya wahalar rayuwa.
Atiku ya ce idan aka zaɓe shi gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali kan manufofin da za su rage tsadar kayayyaki da sufuri, ƙara samar da mai a cikin gida, da kuma sauƙaƙa wa talakawa matsin tattalin arziƙi.














