Da yammacin jiya Alhamis ne kasar Sin ta yi nasarar harba sabon rukunin taurarin dan Adam mai suffar zobi, ta amfani da rokar Long March-2D zuwa sararin samaniya, rukunin taurarin dai shi ne irin sa na farko a duniya da aka taba harbawa sararin samaniyar.
Rukunin mai lakabin PIESAT-1, wanda aka harba da karfe 6 da mintuna 50 na yammaci bisa agogon birnin Beijing, daga tashar harba kumbuna ta Taiyuan dake lardin Shanxi na arewacin kasar Sin, na kunshe da taurarin bil adama 4, za su kuma rika gudanar da ayyukan binciken labarin kasa.
Masana a fannin sun bayyana cewa, rukunin taurarin PIESAT-1, za su rika samar da hidimar bayanan labarin kasa na kasuwanci, da safiyo mai inganci, ta amfani da fasahohin zamani masu nagarta.
Ana aiki da rokar Long March-2D wajen harba taurarin bil adama da nauyin su ya kai tan 1.3, zuwa falakin dake kewaya rana bisa saurin kilomita 700 nesa da doron duniya.
Wannan ne karo na 469 da aka yi amfani da rokar Long March a aikin harba taurarin bil adama na kasar Sin. (Saminu Alhassan)