Da safiyar yau Laraba, kasar Sin ta yi nasarar harba tauraron dan Adam mai nazarin duniyar dan Adam zuwa sararin samaniya, daga cibiyar harba taurari ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar.
An yi amfani da rokar Long March-4C wajen harba tauraron na Gaofen-12 05 ne da misalin karfe 7:45 agogon Beijing, inda ya shiga falakinsa kamar yadda aka tsara.
- Majalisar Dokokin Jigawa Ta Amince Da Ƙudirin Kafa Hukumar Wutar Lantarki
- Xi Ya Bukaci Bunkasa Tsarin Dabarun Soja Na Zamani
Za a yi amfani da tauraron a fannoni daban daban, ciki har da nazarin kasa, da tsare-tsaren birane, da tsarin tituna, da kiyasin albarkatun gona, da agajin jin kai.
Wannan shi ne karo na 540 da aka yi amfani da dangin rokar Long March wajen aiwatar da wannan aiki. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)