Kwamanda a rundunar sojojin ruwan kasar Sin Hu Zhongming, ya jaddada muhimmancin tekun Guinea, yana mai kira ga sassa masu ruwa da tsaki da su hada karfi da karfe, wajen sauya yanayin yankin da tekun yake zuwa yanki na abota, da hadin gwiwa, da wadata da tsaro.
Kwamanda Hu, ya bayyana hakan ne cikin jawabin da ya gabatar, yayin bikin bude wani taron karawa juna sani a yau Laraba a birnin Shanghai, bisa jigon “Tsaro da hadin gwiwa a tekun Guinea”. Ya ce tekun Guinea na da tasiri ba kawai ga yankin da yake ba, har ma ga daukacin kasashen Afirka da duniya baki daya”.
- Gwamna Lawal Ya Jaddada Ƙudurinsa Na Bai Wa Ɓangaren Shari’a ‘Yanci Don Samar Da Adalci A Zamfara
- Sin Ta Gabatarwa MDD Sanarwar Tabbatar Da Shatar Yankinta Na Teku a Tsibirin Huangyan Da Taswirarsa
Kaza lika, jami’in ya ce Sin na jaddada aniyarta, ta yin aiki tare da kasashen dake yankin tekun na Guinea, wajen ingiza samar da zaman lafiya, da daidaito, da ci gaba a yankin.
Taron wanda rundunar sojin ruwa ta ‘yantar da al’ummar kasar Sin ko PLA ta shirya a karo na 2, don tattauna halin da ake ciki a tekun Guinea, ya hallara jagororin rundunar sojin ruwa daga kasashe da dama, da jami’an soji dake ofishin jakadancin kasashe 18, ciki har da na Kamaru, da janhuriyar Congo, da Gabon, Kwadebuwa da Najeriya.
Wannan ne dai karon farko da rundunar PLA ta shirya irin wannan ganawa ta kasa da kasa fuska da fuska, don tattauna batun tsaron yankin tekun Gulf. Ganawar ta biyo bayan makamanciyarta da aka gudanar ta yanar gizo a shekarar 2022, inda mahalarta taron suka yi musayar ra’ayoyi don gane da tarin kalubalen tsaron teku, karkashin manufar samar da “Al’umma mai makomar bai daya ta fuskar tsaron teku.” (Mai fassara: Saminu Alhassan)