A ranar 9 ga wata bisa agogon wurin, yayin biki mai taken “Natural Day” na babban taron kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo 28 COP28 da ake gudanar a birnin Dubai na hadaddiyar daular Larabawa, kasar Sin ta sanar da shiga kungiyar “ High Ambition Alliance for Nature and Humanity” a hukumance, inda ta jagoranci kaddamar da shirin aiki na “Kunming-Montreal Global Diversity Framework”.
A yayin bikin, shugaban babban taron sassan da suka amince da yarjejeniyar kare mabambantan halittu karo na 15, kuma ministan kula da muhalli na kasar Sin, Huang Runqiu ya bayyana ta kafar bidiyo cewa, matsalar sauyin yanayi da yadda ake asarar mabambantan halittu, suna haifar da babban kalubale ga rayuwa da ma ci gaban bil-Adama. Kasar Sin na fatan babban taron na COP28, zai aiwatar da hadin gwiwa tsakanin bangarori da dama bisa gaskiya, tare da samun sakamako mai kyau da kuma inganci.
- Hangzhou: An Gudanar Da Taron Dandalin Tattaunawar Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Kan Shirye-shiryen Rediyo Da Telebijin Karo Na 6
- Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Da Kin Amincewar Amurka Da Kudurin Tsagaita Wuta Domin Jin Kai
Huang Runqiu ya kuma yi kira ga dukkan bangarorin da su gaggauta yin kwaskwarima ga “manyan tsare-tsare da shirin ayyukan kiyaye mabambantan halittu”, da kuma tattara karin albarkatu, don kara azama kan cimma manyan manufofi guda uku na yarjejeniyar kare mabambantan halittu bisa daidaito.
Kasar Sin tana maraba da dukkan masu ruwa da tsaki, da su taka rawar gani wajen gudanar da harkokin kula da mabambantan halittu, kuma tana matukar yabawa da goyon bayan dukkan alkawura da tsare-tsare da hadin gwiwar da suka dace, wajen sa kaimi ga aiwatar da tsarin aikin Kunming-Montreal.
Kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kasashen duniya, wajen tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta kamar hasarar rabe-raben halittu da matsalar sauyin yanayi, tare da sa kaimi ga cimma nasarar gudanar da babban taron bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo na 28 COP28, domin samar da duniya mai kyau inda za a samu zaman jituwa tsakanin mutum da yanayi.
Sannan, a yayin taron manema labaru na farko da tawagar kasar Sin mai halartar babban taron kasashen duniya da suka sanya hannu kan yarjejeniyar MDD kan sauyin yanayi karo na 28 COP28 ta gudanar a jiya, manzon musamman mai kula da harkokin sauyin yanayi na kasar Sin Xie Zhenhua ya yi bayani game da nasarorin da Sin ta samu wajen canja tsarin raya kasa tare da kiyaye muhalli da raya makamashin da za a iya sabuntawa. Xie ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasa da kasa wajen tinkarar sauyin yanayi.
Xie Zhenhua ya bayyana cewa, kasar Sin ta samar da babbar gudummawa wajen kyautata tsarin samar da makamashi da raya makamashin da za a iya sabuntawa. Ya zuwa yanzu, yawan kudin da aka kashe wajen samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da karfin iska ya ragu da kashi 80 cikin dari, yawansu ta hanyar hasken rana ya ragu da kashi 90 cikin dari, wadanda suka aza tubalin yin amfani da irin wannan makamashi a fadin duniya. A halin yanzu, yawan na’urorin samar da makamashin da za a sabuntawa ya fi yawan na kwal, wannan wani babban canji ne a tsarin samar da makamashi. Sin za ta ci gaba da yin amfani da makamashin da za a iya sabuntawa don maye gurbin makamashin kwal da sauran burbushin halittu.
Wakilin Sin ya kara da cewa, Sin ta hada kai da kasashe da yankuna fiye da 100, kan ayyukan samar da makamashi masu tsabta, da daddale yarjejeniyoyin fahimtar juna kan hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa wajen tinkarar sauyin yanayi tare da kasashe masu tasowa fiye da 10. A nan gaba Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasashe masu tasowa don inganta hadin gwiwarsu a fannonin kudi da fasahohi. (Ibrahim Yaya, Zainab Zhang)