An gudanar da taron kafa kungiyar masana masu binciken sararin samaniya mai zurfi ta kasa da kasa wato IDSEA a birnin Hefei dake lardin Anhui, yau Litinin. Wannan ita ce kungiyar masana kimiyya da fasaha ta kasa da kasa ta farko da kasar Sin ta kafa a fannin binciken sararin samaniya mai zurfi.
A cikin watan Afrilun bana ne majalisar gudanarwar kasar Sin ta amince da kafa kungiyar IDSEA, wadda kungiyoyi guda 5 suka ba da shawarar kafa ta tare, ciki har da cibiyar binciken duniyar wata da ayyukan binciken sararin samaniya ta hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin, da cibiyar binciken sararin samaniya ta kasar Faransa mai suna “Planetary Exploration, Horizon 2061.” Kuma ta zama wata kungiya mai zaman kanta ta kasa da kasa a fannin kimiyya da fasaha da ta yi rijista da hukumar da batun ya shafa.
Wu Weiren, babban mai tsara aikin binciken duniyar wata na kasar Sin, ya bayyana cewa, kafa wannan kungiyar na da matukar muhimmanci kan mu’amala da hadin gwiwar sararin samaniya tsakanin Sin da kasa da kasa. Ana gayyatar masana kimiyya da injiniyoyi daga fagen binciken sararin samaniya da kimiyya da fasaha na duniya don shiga cikin kungiyar, da ba da kyakkyawar gudummawa ga binciken sirrin sararin samaniya.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp