A yau Alhamis, ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce kasar ta kara wasu sassa 28 na kasar Amurka, cikin jerin wadanda ta sanyawa takunkumin hana shigar musu da kayayyaki. Sassan sun hada da kamfanonin General Dynamics, da Boeing Defense, da Space & Security, da sauran su.
Hakan a cewar ma’aikatar, mataki ne na tabbar da tsaron kasa da moriyarta, da burin dakile bazuwar makamai, da sauran wasu nauyaye-nauyaye na kasa da kasa.
- Dokar Haraji Za Ta Ƙara Jefa Al’umma Cikin Talauci – Gwamnatin Kano
- Ɓaraka:, Ƴan Adawa, Shugabannin APC Na Shirya Kafa Sabuwar Tafiya — Lukman
Kaza lika, Sin ta ayyana sunayen wasu kamfanonin Amurkan 10, cikin jerin sassan da ba za a iya dogaro da su ba, bisa sayarwa yankin Taiwan na Sin makamai. Kamfanonin sun hada da Lockheed Martin Missiles, da Fire Control, da Lockheed Martin Aeronautics, da Lockheed Martin Missile System Integration Lab.
Bisa wannan mataki, Sin ta haramtawa wadannan kamfanoni duk wasu harkoki da suka shafi shigarwa, ko fitar da kayayyaki daga Sin, tare da hana su zuba sabbin jari a kasar Sin. (Saminu Alhassan)
yau Alhamis, ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce kasar ta kara wasu sassa 28 na kasar Amurka, cikin jerin wadanda ta sanyawa takunkumin hana shigar musu da kayayyaki. Sassan sun hada da kamfanonin General Dynamics, da Boeing Defense, da Space & Security, da sauran su.