Yau Laraba, ma’aikatar masana’antu da sadarwa ta kasar Sin, tare da sauran hukumomin da abin ya shafa, sun fitar da wani daftari mai taken “Jagora ga aiwatar da kawo sauyi na fasahar zamani ga masana’antun kere-kere”, wanda ya bayar da shawarar kara wa kamfanoni kwarin gwiwa wajen gudanar da bincike da aiwatar da sabbin ayyuka masu amfani da fasahohin zamani, da kuma samar da manhajoji na ajin gaba a kan kirkirarriyar basira da aka yi wa lakabi da “AI+”.
Daftarin ya kuma ba da shawarar cewa, ya kamata a kara wa biranen kasar kwarin gwiwa don su iya dogaro da sabbin yankunan masana’antu na gwaji a fannin fasaha da kuma yankunan gwaji da aka kebe na kawo sauye-sauyen fasahar zamani ga kanana da matsakaitan kamfanoni, wajen tsara taswirar kawo sauye-sauyen fasaha na kamfanoni, da tabbatar da inganci, da sabunta na’urorin aiki da daidaita samarwa da bukatu, ta yadda za a samu damar ba da tallafin kudi ga bangaren kawo sauye-sauyen zamani ga masana’antun kere-kere. (Safiyah Ma)