Ma’aikatar tsaro ta kasar Sin, ta ce matakan martani da ta dauka dangane da ziyarar kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi a Taiwan, matakai ne da suka wajaba domin gargadin Amurka da Taiwan game da takalar Sin.
Kakakin ma’aikatar Wu Qian, ya ce matakan halaltattu ne da suka dace da tsaron kasar da yankunanta.
Wu ya bayyana haka ne a makon da ya gabata, yayin da kafafen yada labaran Amurka ke cewa, Sin ta ki amsa kiran shugaban ma’aikatar tsaron Amurka wato Pentagon.
A cewar Wu Qian, dole ne Amurka ta dauki alhakin da duk wani abun da zai biyo baya, saboda tsokanar Sin, yana mai zargin Amurkar da haifar da yanayin zaman dar dar a zirin Taiwan. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp