Dangane da kalaman da ministar tsaron kasar Canada Anita Anand ta yi a yayin taron tattaunawa na Shangri-La kan abin da ake kira wai “jirgin sojojin kasar Sin ya sa gaban jirgin sojan yakin Canada”, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin ya bayyana Litinin din nan cewa, ikirarin da abin ya shafa na kasar Canada kan kasar Sin, neman kare kai ne kawai.
Wang Wenbin ya ce, kasar Canada ta yi ikirarin cewa, jirigin yakinta yana martaba kudurin kwamitin sulhu na MDD kan takunkumin da aka kakaba wa kasar Koriya ta Arewa (DPRK), amma kudurorin kwamitin sulhun MDD da abin ya shafa, ba su ba wata kasa damar tura dakarun soji cikin yankin ruwa da sararin samaniya a karkashin ikon wasu kasashe, don gudanar da ayyukan sa ido ba.
Abin da jirgin saman sojan kasar Canada ya aikata, ba komai ba ne illa tsokanar kasa mai cin gashin kanta.
Don haka, Wang ya bukaci bangaren Canada, da ya mutunta hakikanin shaidu, da nisantar cin zarafin kasar Sin, da gaggauta daina yada labaran karya, da kuma dakatar da duk wani mataki da ka iya kawo cikas ga ‘yancin kai da tsaron kasar Sin, da sunan aiwatar da kudurorin kwamitin sulhu na MDD.(Ibrahim)