Kwanan baya, ma’aikatar kasuwanci ta Amurka, ta fitar da wata sanarwa game da gyaran manufarta ta kayyade fitar da kayayyakin sassan na’urorin laturoni na “Semiconductor” zuwa ketare, wadda ta gabatar a ranar 17 ga watan Oktoban shekarar 2023 da ta gabata.
Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya mai da martani a jiya Lahadi, inda ya ce Sin ta lura da wannan gyara, wanda ya zo kasa da rabin shekara, tun bayan da Amurka ta gabatar da manufa.
Jami’in ya kara da cewa, kamfanonin kasa da kasa ciki har da na Amurka, suna bukatar wani yanayi mai dorewa dake da makoma mai haske. Sai dai Amurka ta gyara manufofi yadda take so, ta fakewa da batun tsaron kasa, matakin da ba kawai na gurgunta hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki tsakanin kamfanonin kasashen biyu kadai ba ne, har ma ya haddasa rashin tabbaci ga sana’ar samar da kayan laturoni masu amfani da “Semiconductor” ta duniya. (Amina Xu)