Jakadan Sin kan kwance damara Shen Jian ya yi jawabi a taron kwamiti na farko na babban taron MDD kan batun rage makaman nukiliya a jiya cewa, wasu kasashe ciki har da kasar Amurka sun sake zargin manufofin nukiliya na kasar Sin, ya jaddada cewa, Amurka ce ta fi aikata laifuffuka da suka shafi makaman nukiliya.
Shen Jian ya bayyana cewa, ya kamata kasar Amurka ta dakatar da murde gaskiya kan manufofin nukiliya na kasar Sin. Kasar Sin ta kiyaye manufar hana fara yin amfani da makaman nukiliya har na tsawon shekaru 60. A kwanakin baya, kasar Sin ta sake ba da shawara a hukumance cewa, kasashen dake mallakar makaman nukiliya su yi shawarwari kan daddale yarjejeniyar hana fara yin amfani da makaman nukiliya a kan juna, ko kuma bayar da sanarwar siyasa game da batun.
Shen Jian ya kara da cewa, ya kamata kasar Amurka ta dakatar da yada jita-jita kan yadda Sin ta kara yawa makaman nukiliya. Kasar Sin ta kiyaye yawan makaman nukiliya bisa bukatun kiyaye tsaron kasar, a baya da kuma a nan gaba ba za ta shiga takara kan makaman nukiliya ba. Kasar Amurka tana yada labaran bogi game da yawan makaman nukiliya na kasar Sin, da kara gishiri kan cewa ana fuskantar barazanar aikin soja daga kasar Sin, yunkurinta shi ne bayar da dalilai don karfafa kawancen aikin sojanta, da hana bunkasuwar kasar Sin, da kuma neman samun moriyar kamfanonin masana’antun soja na kasar Amurka. (Zainab Zhang)