Zaunanen wakilin kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya Fu Cong, ya mika wata wasika ga babban magatakardan Majalisar Antonio Guterres, don bayyana ra’ayin gwamnatin kasar Sin, dangane da furucin firaministar kasar Japan Takaichi Sanae mai cike da kura-kurai.
Cikin wasikar da wakilin na Sin ya mika a jiya Juma’a, an bayyana kalaman Takaichi dangane da yankin Taiwan na Sin, a matsayin karon farko tun bayan da kasar Japan ta ba da kai a yakin duniya na 2 a shekarar 1945, da kasar ta bayyana yunkurinta na tsoma baki cikin batun Taiwan na Sin ta hanyar daukar matakan soja, wanda hakan ya kasance barazana ga kasar ta Sin. Kuma tabbas idan har Japan ta tura sojoji bisa dalilin wai “kare yankin Taiwan”, hakan zai zama tamkar kaiwa kasar Sin hari ne, lamarin da zai sa kasar Sin daukar kwararan matakai na kare kanta.
Ban da haka, duk a jiya Juma’a, yayin taron wata-wata na hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa, wakilin Sin a hukumar Mista Li Song, ya ce kamata ya yi a tsaurara matakan sanya ido kan kasar Japan, bisa la’akari da yiwuwar kasar ta yi watsi da alkawuranta na magance mallakar makaman nukiliya. (Bello Wang)














