Zaunannen wakilin Sin dake MDD Fu Cong ya bayyana a gun taron gaggawa don tattauna yanayin da kasashen Lebanon da Isra’ila ke ciki na kwamitin sulhun MDD a jiya cewa, kasar Sin ta nuna damuwa ga yadda yanayi ya tsananta a tsakanin kasashen biyu, kana ta yi kira ga bangarori daban daban da su kai zuciya nesa.
Fu Cong ya bayyana cewa, Sin ta nuna damuwa sosai kan fashewar bama-bamai a cikin dubban na’urorin sadarwa a Lebanon, lamarin da ya haddasa mutuwa da jikkata dubban jama’ar Lebanon. Wannan aiki ya sabawa ikon mallaka da tsaron kasa da kuma dokokin kasa da kasa, musamman dokar jin kai ta duniya, kana ya yi watsi da rayuwar jama’a. Ya zama dole a yi Allah wadai da wannan danyen aiki.
- Nazari Kan Dabarun Koyarwa Da Amfaninsu (6)
- Farashin Kayan Amfanin Gona Ya Fara Sauka A Wasu Kasuwanni
Kwamitin sulhun MDD ya gudanar da taro kan batun cikin gaggawa a jiya, inda aka tattauna sabon yanayin da ake ciki a Lebanon. Wakilai masu halartar taron sun yi kashedin cewa, sabon harin da aka kaiwa Lebanon na alamta ta da sabon yaki, kuma sun yi kira ga bangarori daban daban da su dakatar da ta da rikici tsakanin juna.
Ministan kiwon lafiya na Lebanon Dr. Firass Abiad ya bayyana a ran 19 ga wata cewa, lamarin tashin bama-bamai a cikin na’urorin sadarwa da ya auku a ranar 17 da 18 ga wata a kasar ya haddasa mutuwar mutane 37 tare da raunata mutane 2931. (Zainab Zhang)