A kwanakin baya, an bude tashar jirgin ruwa ta fasinja ta kasa da kasa ta kasar Sin ta farko, wato tashar jirgin ruwa ta Shekou dake birnin Shenzhen. ’Yan kasuwa daga Argentina, da Chile, da Brazil sun shiga kasar Sin ta tashar bisa sabuwar manufar shiga kasar Sin ba tare da biza ba, inda aka rage lokacin daidaita aikin canza jirgi daga awoyi biyu da rabi zuwa kasa da rabin awa. Wannan ya shaida cewa, an aiwatar da manufar shiga kasar Sin ba tare da biza ba, ba ma kawai a filin jirgin sama ba, har ma a tashar jirgin ruwa. Hakan ya hanzarta raya cinikayyar Sin da kasashen waje.
Wannan batu ya kasance wani misali, bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar shiga kasar Sin ba tare da biza ba. A cikin shekaru 5 da suka gabata, wato cikin wa’adin aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar na raya kasar Sin na 14, gwamnatin kasar ta kara kyautata manufofin shiga kasar ba tare da biza ba a fannoni daban daban, don sa kaimi ga yin mu’amala tare da sauran sassan kasa da kasa.
A halin yanzu, kasar Sin ta bada damar shiga kasar ba tare da biza ba ga kasashe 75, inda yawan kasashen da suke da izinin ratsa kasar Sin ba tare da biza ba ya karu zuwa 55, kana yawan tasoshin bincike dake kan iyakar kasar Sin da sauran kasashe makwabta, inda ake iya shiga kasar Sin ba tare da biza ba ya karu zuwa 60, kana tsawon lokacin da ake iya yada zango cikin kasar ya karu zuwa awoyi 240, wanda hakan ya kawo sauki ga al’ummun kasashen waje, dake zuwa kasar Sin don yawon shakatawa, da yin ciniki da kuma yin ziyara.
Manufofin shiga kasar Sin ba tare da samun biza ba sun shaida cewa, Sinawa suna son baki tun a da can, kuma gwamnatin kasar Sin ta yi imani da fadada bude kofa ga kasashen waje. A shekaru 5 masu zuwa, Sin tana maraba da karin al’ummun kasashen waje da za su shiga kasar Sin, da ganewa idanunsu yanayin kasar da kuma fahimtarta. Kazalika, hakan zai kara shaida cewa, bunkasar kasar Sin na da nasaba da duniya, kana wadatar duniya tana bukatar kasar Sin baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp