Jiya Asabar, cibiyar nazarin raya kasa ta majalisar gudanarwar kasar Sin, da hukumar kula da kadarorin kasar, da sauran hukumomin da abin ya shafa na kasar, sun kaddamar da taron dandalin tattauna hanyoyin amfani da makamashi na kasa da kasa, na shekarar 2023 a birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, inda aka fitar da “Rahoton ci gaban juyin juya halin makamashin kasar Sin”, wanda ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta samu babban ci gaba, wajen amfani da makamashi a cikin shekaru goma da suka gabata.
Rahoton ya nuna cewa, tun daga shekarar 2012, kasar Sin ta yi kokarin kyautata hanyoyin amfani da makamashi domin kiyaye muhalli. Ya zuwa shekarar 2022, kwatankwacin adadin kwal mai inganci da aka yi amfani da su a kasar Sin, ya karu da tan biliyan 1.39 bisa na shekarar 2012, wato ya karu da kaso 3 bisa dari ke nan a ko wace shekara daya, amma adadin GDPn kasar ya karu da kaso 6.2 bisa dari.
A sa’i daya kuma, adadin iskar carbon da kasar ke fitarwa sakamakon ayyukan masana’antu a shekarar 2022, ya ragu da kaso 40.1 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekarar 2012. Don haka ana iya cewa, an rage yawan makamashi masu illa ga muhalli da aka yi amfani da su yadda ya kamata, kuma an samu sakamako mai kyau a fannin amfani da sabbin makamashi masu tsabta, tare kuma da kyautata tsarin amfani da makamashi a kasar.
Kana rahoton ya yi bayani, game da yadda za a yi amfani da makamashi a kasar Sin a cikin shekaru goma masu zuwa. (Mai fassara: Jamila)