Kamfanin sufurin jiragen kasa na kasar Sin ya sanar da cewa, a cikin watanni bakwai na farkon shekarar 2025, kasar ta samu bunkasar jigilar kayayyaki ta jiragen kasa a-kai-a-kai bisa karin layukan zirga-zirga da kuma ingantattun ayyuka.
Kamfanin ya bayyana cewa, an gudanar da jigilar kayayyaki sama da tan biliyan 2.33 a layukan dogo na cikin kasa a tsakanin wannan lokacin, wanda ya nuna an samu karuwar kashi 3.3 bisa dari a mizanin duk shekara. A bangaren jigilar kayayyaki ta motoci kuwa, matsakaicin adadin jigilar da aka gudanar na mizanin kullum ya tasamma 183,300, wanda ya karu da kashi 4.1 idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara.
Har ila yau, shi ma bangaren jigilar kayayyaki na kasa da kasa ya nuna hazaka ba tare da tangarda ba, inda aka gudanar da jimillar zirga-zirgar jiragen kasa na dakon kaya zuwa yankin Tsakiyar Asiya 8,526, wanda ya karu da kashi 23.2 cikin dari a kan na shekarar da ta gabata. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp