An yi balaguro na cikin gida sama da biliyan 3.28 a kasar Sin a rabin farko na shekarar 2025, adadin da ya karu da kashi 20.6 cikin dari a mizanin duk shekara, bisa bayanan da ma’aikatar al’adu da yawon bude ido ta fitar a yau Jumma’a.
Masu yawon bude ido na cikin gida sun kashe jimillar yuan tiriliyan 3.15 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 441 a cikin wadannan watanni shida, inda adadin ya karu da kaso 15.2 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar 2024.
Bugu da kari, musamman an lura da yadda yawan tafiye-tafiyen cikin gida da mazauna yankunan karkara ke yi suka karu da kashi 30.6 cikin dari a mizanin duk shekara, inda aka samu karin kashi 30.1 cikin dari idan aka kwatanta da na rabin farkon bara. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp