Ministan harkokin cinikayya na kasar Sin Wang Wentao ya bayyana cewa, a matsayinta na kasar dake kan gaba a fannin cinikayya a duniya, kasar tana kuma kara samun ci gaba wajen cimma burinta na zama kasar da babu kamarta a fannin kasuwanci mai inganci.
Wang, wanda ya bayyana haka yayin da yake gabatar da rahoto na musamman kan ci gaban cinikayyar waje na kasar, a yayin wani taron karawa juna sani kan yanayin tattalin arzikin kasar da aka gudanar a birnin Beijing, fadar mulkin kasar, ya bayyana cewa, cinikayyar waje ta kasar Sin, ta jure matsin lamba a shekarar 2023, yayin da ma’auni da kuma karfinta a harkokin cinikayyar duniya gaba daya ba su sauya ba.
A halin da ake ciki kuma, tsarin cinikayyar waje na kasar, ya kara inganta, baya ga kara samun abokan hulda daban-daban a shekarar 2023, matakin dake nuna juriyar da tattalin arzikin kasar yake da shi. (Mai fassara: Ibrahim)