Mizanin hayakin carbon da ake fitarwa sakamakon ayyukan bil’adama a kasar Sin, ya daga da kaso 0.6 bisa dari a shekarar 2024 da ta gabata, adadin da ya shaida karancin karuwar alkaluman, idan an kwatanta da na shekarar da ta gabaci hakan, kana ya yi kasa da na matsakaicin matsayi da sauran sassan kasa da kasa suka fitar.
A jiya Laraba ne hukumar hasashen yanayi ta kasar Sin ko CMA, ta sanar da cewa, kokarin da ake yi na cika alkawuran kasar Sin dangane da sauyin yanayi na samun tagomashi. Hukumar ta ce alkaluman da aka fitar dangane da mizanin yawan fitar da nau’o’in hayaki masu dumama yanayi na 2024, sun nuna kyakkyawan mataki da Sin ke ciki na karuwar kaso 0.6 bisa dari, kasa da karuwar kaso 0.8 bisa dari da sauran kasashen duniya ke ciki.
Dangane da hakan, daraktan sashen kimiyya da fasaha a hukumar ta CMA Zeng Qin, ya ce hakan ya shaida yadda ayyukan Sin na cika alkawuranta, dangane da rage fitar da hayakin carbon ke haifar da manyan nasarori. (Mai fassara: Saminu Alhassan)














