Cikin shekarar 2024, an kafa sabbin kamfanonin 59,000 masu jarin waje a kasar Sin, adadin da ya karu da kaso 9.9 bisa dari kan na 2023.
Wani rahoto da ma’aikatar kula da cinikayya ta Sin ta fitar a wajen bikin baje kolin cinikayya da zuba jari karo na 25 dake gudana a birnin Xiamen ya ce, ainihin jarin waje da aka yi amfani da shi a kasar a bara ya kai dala biliyan 116.24, lamarin da ya sa kasar ta ci gaba da rike matsayinta na mafi samun jarin waje a tsakanin kasashe masu tasowa.
Haka kuma, ana ci gaba da samun ingantuwar bangarorin da ake zubawa jarin waje a kasar, inda masana’antar fasahohin zamani ta dauki kaso 34.6 na jimilar jarin. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp