Albarkacin ranar yaki da miyagun kwayoyi ta kasa da kasa, ofishin dakile miyagun kwayoyi na kasar Sin ya gabatar da rahoton halin da kasar take ciki a wannan bangare, inda alkaluma suka nuna cewa, a shekarar 2024, hukumomi masu alaka sun binciki laifuka masu nasaba da miyagun kwayoyi fiye da dubu 37, da cafke masu aikata laifukan dubu 62, baya ga kama miyagun kwayoyi ton 26.7. Adadin laifuka masu nasaba da miyagun kwayoyi da aka bincika ya ragu da kashi 12.9%, yayin da yawan masu aikata laifukan da aka cafke ya ragu da kashi 5.6% bisa na makamancin lokacin a shekarar 2023.
Ban da wannan kuma, Sin ta yi kokarin sauke nauyin dake wuyanta, inda ta shiga a dama da ita a hadin gwiwar kasa da kasa a bangaren yaki da miyagun kwayoyi. Kuma a matsayin kasar da ta kulla yarjejeniyar yaki da miyagun kwayoyi ta MDD, Sin ta yi kokarin sa hannun aikin tsara dokokin yaki da miyagun kwayoyi na duniya, da samar da dabaru da gudummawarta a wannan bangare.
Kazalika, a matsayin daya daga kasashen da suke fi daukar tsauraran matakan yaki da miyagun kwayoyi a duniya, kasar Sin ta bayyana niyyarta ta haramta miyagun kwayoyi bisa hakikanin matakan da ta dauka, wanda hakan ba alkawari take yi ga jama’arta ba kadai, haka kuma ya amsa bukatun jama’ar duniya. Matsayin da Sin ta dauka a wannan bangare yana kuma karfafa sauran kasashe gwiwar samun nasarar yaki da miyagun kwayoyi a duniya baki daya. (Mai zane da rubutu: MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp