Gwamnatin kasar Sin ta shata, tare da sanar da kewayen yankinta na teku daura da tsibirin Huangyan, matakin da sananne ne bisa doka a fannin karfafa tsarin gudanarwa, ya kuma dace da dokokin kasa da kasa, da ayyukan da aka saba gudanarwa.
Da yake tabbatar da hakan a Lahadin nan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Sin, ya ce tun asali tsibirin Huangyan bangare ne na yankunan kasar Sin. Kuma bisa dokokin kasa da kasa, kamar yarjejeniyar MDD game da teku, da dokar janhuriyar jama’ar kasar Sin mai nasaba da yankunan teku da yanki mai makwaftaka, gwamnatin kasar Sin ta shata wannan iyaka, tare da sanar da sassan kan iyakar yankinta na teku daura da tsibirin Huangyan.
A nata bangare, rundunar tsaron teku ta kasar Sin ko CCG, ta bayyana cewa, za ta ci gaba da zage damtse wajen karfafa sintiri, da tabbatar da kare doka a yankunan ruwa daura da tsibirin Huangyan na Sin, da ma sauran yankunan ruwa mallakin kasar. (Mai fassara: Saminu Alhassan)