Kasar Sin tana fatan samar da na’urorin da ake kira virtual reality (VR) miliyan 25 nan da shekarar 2026, kamar yadda wani shiri game da bunkasa fasahar ta VR da aka fitar Talatar nan ya bayyana.
Wani shiri na hadin gwiwa da ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa da wasu sassa hudu da abin ya shafa suka fitar tare, ya nuna cewa, darajar masanan’antar VR na kasar Sin da suka hada da manya da kananan na’urori da wadanda ake sarrafawa, za ta zarce Yuan biliyan 350, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 48.1 nan da shekarar 2026. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)