Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya sanar da kakabawa mataimakiyar ministan sufuri da sadarwa na kasar Lithuania Agne Vaiciukeviciute takunkumi.
Hakan dai ya biyo bayan ziyarar da jami’ar ta kai yankin Taiwan, lamarin da ya keta alfarmar manufar kasar Sin daya tak a duniya, tare da tsoma baki cikin harkokin gidan kasar, da keta hurumin mulkin kai, da tsaron yankunan kasar Sin.
Takunkumin da kasar Sin ta kakabawa Vaiciukeviciute, ya hada da dakatar da dukkanin wata musaya, tsakanin bangaren Sin da ma’aikatar da jami’in ke wakilta, da kuma jingine duk wata hadin gwiwa da musaya da Lithuania, a fannonin sufurin hanyoyin mota na kasa da kasa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp