• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Ta Sauke Nauyin Dake Wuyanta Wajen Taimakawa Kasashen Da Suka Fi Rashin Ci Gaba

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

Daga ran 1 ga wata, kasar Sin ta cire haraji kan kaso 98 cikin 100 na nau’o’in kayayyakin da take shigo da su daga wasu kasashen da suka fi rashin samun ci gaba guda 10, ciki hadda Benin da Burkina Faso da Guinea Bissau da Tanzaniya da Uganda da Zambiya da sauransu. Kawo yanzu dai, gaba daya kasashe 26 na amfana da wannan manufa. Yau “duniya a zanen MINA” zai bayyana muku wannan manufa mai kyau da ma yadda Sin ta sauke nauyin dake wuyanta na taimakawa kasashen da suka fi rashin samun ci gaba.

Wannan manufa ta baiwa kasashen damar fitar da kayayyakinsu zuwa kasuwar kasar Sin mai girma ba tare da biyan haraji ba. A hakika, tun daga shekarar 2008, Sin ta yi ta kara kayayyaki da kasashen da za su amfana da wannan manufa.

  • Sahihanci Shi Ne Tushen Hadin Gwiwar Afirka Da Sin

Ya zuwa yanzu, kasashe 26 da suka kulla yarjejeniyar rashin biyan haraji kan kayayyaki na kaso 98 cikin 100 da za su shigar Sin, 18 daga cikinsu kasashen Afrika ne. Alkaluma na nuna cewa, yawan kudin dake shafar ciniki tsakanin Sin da Afrika a shekarar 2021 ya karu da kashi 25.3% bisa na makamancin lokaci na 2020, daga cikinsu darajar yawan kayayyakin Afirka da suka shiga kasuwar Sin ya kai dala biliyan 105.9, wanda ya kai wani sabon matsayi a tarihi.

Yadda kasashen suke iya fitar da kayayyakinsu kasuwar kasar Sin ba tare da biyan kudin haraji ba, ya taimakawa al’ummar wadannan kasashe wajen samun aikin yi da jawo jarin waje a wasu sha’anoni da ma ingiza samun bunkasuwa cikin daidaito da sauransu.

Masu iya magana na cewa, ka so wa dan uwanka abin da ka so wa kanka. Sin ta dade tana sauke nauyin dake wuyanta na taimakawa kasashen da suka fi rashin samun ci gaba a duniya, da kara ba su damar fitar da kayayyakinsu kasuwannin kasar Sin. Abin dake da muhimmiyar ma’ana ga hadin kansu a fannin kawar da talauci da cin moriyar juna da more kyakkyawar makoma tare.

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

An yi imanin cewa, hadin kan Sin da Afrika zai amfanawa al’umomin bangarorin biyu. Sin tana kokarin cika alkawarinta na taimakawa kasashe da suka fi rashin samun ci gaba, matakin dake bayyana niyyar Sin a bangaren samun bunkasuwa tare da rungumar kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya da sauran kasashe. (Mai zane da rubuta: MINA)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki
Daga Birnin Sin

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
Daga Birnin Sin

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Next Post
Portugal Ko Switzerland, Wa Za Ta Kai Bantenta Bayan Morocco Ta Lallasa Spain?

Portugal Ko Switzerland, Wa Za Ta Kai Bantenta Bayan Morocco Ta Lallasa Spain?

LABARAI MASU NASABA

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025
Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

November 6, 2025
Garkuwa: Sarkin Gobir Ya Bukaci Agajin Gaggawa Daga Gwamnatin Sakkwato

An Kama Wani Mutum Kan Zargin Kashe Matarsa A Sakkwato

November 6, 2025
Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Don Karɓo Rancen N1.15trn Don Cike Giɓin Kasafin Kuɗin 2025

November 6, 2025
Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

November 6, 2025
Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

November 6, 2025
Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

November 6, 2025
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP

Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro

November 6, 2025
Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.