Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkanin sassa, wajen shawo kan duk wata takaddama da ka iya jefa tekun Red Sea cikin tashin hankali.
Kaza lika Sin na fatan shiga a dama da ita wajen warware batutuwan da suka shafi kasar Yemen ta hanyar siyasa, da cimma nasarar tsagaita bude wuta a Gaza, da wanzar da zaman lafiya da daidaito mai dorewa a Gabas ta Tsakiya.
- Kasashen Afirka Na Fadada Cudanya Da Kasar Sin A Fannoni Daban Daban
- Masu Fyade Da ’Yan Luwadi 369 Aka Kama A 2023 A Katsina
Geng, wanda ya bayyana hakan yayin taron gaggawa na kwamitin tsaron MDD a jiya Laraba, wanda ya maida hankali ga tattauna yanayin da ake ciki a tekun Red Sea, ya kara da cewa, tekun na da matukar muhimmanci ta fuskar sufurin hajoji da makamashi, kuma tabbatar da kyakkyawan yanayin gudanar ruwan sa, da tsaron jiragen dake sintiri a cikin sa, ba kawai zai taimakawa zaman lafiya da daidaito a yankin da yake ba ne kadai, har ma hakan zai taimaka wajen wanzar da safarar hajoji tsakanin sassan duniya, da kare tsarin cinikayyar kasa da kasa.
Har ila yau, matakin zai haifar da gajiyar bai daya ga sassan kasa da kasa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)