Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace, don kiyaye hakki da muradun kamfanonin kasar, idan har kasar Amurka ta kakaba takunkumi kan kamfanoninta, ta hanyar fakewa da wai suna yin hadin gwiwa da kasar Rasha.
Kalaman nata na zuwa ne, bayan wasu rahotannin kafafen yada labarai na cewa, Amurka na duba yiwuwar kakabawa kamfanonin Sin takunkumin da ta yi imanin cewa, suna taimakawa Rasha rura wutar rikicin Ukraine.
- Karo Na Farko Ne CIDCA Da Hukumar MDD Da Habasha Sun Sa Hannu Kan Takardar Hadin Gwiwa Da Ta Shafi Bangarori Uku
- Jirgin C919 Na Sin Ya Halarci Bitar Bikin Nune-nune Jiragen Sama Na Singapore
Mao ta shaidawa taron manema labarai na yau da kullum cewa, Sin a ko da yaushe tana goyon bayan gaskiya da matsayi na adalci don inganta tattaunawar zaman lafiya kan rikicin Ukraine.
Ta kara da cewa, kasar Sin na da ‘yancin yin hadin gwiwa tare da sauran kasashe kamar yadda ta saba, kuma tana adawa da kakaba takunkumi na kashin kai da ikon kotu na kakaba takunkumi kan wani kamfani saboda ya gudanar da kasuwanci a wata kasa, wadanda ba su da tushe a cikin dokokin kasa da kasa, kuma ba su samu izni daga kwamitin sulhu na MDD ba.(Ibrahim)