• English
  • Business News
Saturday, October 18, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Ta Shafe Shekaru 60 Tana Aikewa Da Ma’aikatan Agajin Jinya Zuwa Kasashen Waje

by Sulaiman
2 years ago
Sin

A farkon shekarun 1960, ba da jimawa ba da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin, wadda ke bukatar ci gaba, kuma ba ta da arziki sosai. Amma a lokacin, kasar Aljeriya da ta samu ‘yanci bada dadewa ba, ta yi kira ga sassan kasa da kasa ta kungiyar bada agaji ta Red Cross ta duniya, da su samar mata da tallafin jinya na gaggawa. Sin ce kasa ta farko da ta fito fili ta sanar da tura kwararrun likitocinta zuwa Aljeriya. Watakila kasashen duniya ba su taba tsammanin cewa, kasar Sin za ta shafe tsawon shekaru 60 tana gudanar da wannan aiki ba.

Nasarorin da kasar Sin ta samu cikin shekaru 60 a fannin samar da agajin jinya ga kasashen waje, sun baiwa dukkanin duniya zarafin fahimtar nauyin dake wuyan kasar. Sin kasa ce daya kadai a duk fadin duniya, da ke tsayawa wajen aikewa da tawagogin ma’aikatan agajin jinya zuwa kasashe masu tasowa cikin dogon lokaci.

  • Shugabannin Sin Sun Kalli Wasan Gargajiya Na Opera Domin Maraba Da Sabuwar Shekarar 2024
  • Samar Da Tsaro: Ribadu Ya Yaba Wa Sarakunan Gargajiya A Adamawa

Kawo yanzu, kasar Sin ta riga ta tura ma’aikatan samar da agajin jinya sama da dubu 30 zuwa kasashe da yankuna 76, da bada tallafin gina cibiyoyin likitanci da kiwon lafiya sama da 130, kuma adadin marasa lafiyar da likitocin kasar Sin suka kula da su ya tasam ma miliyan 300.

Bugu da kari, ma’aikatan samar da agajin jinya na kasar Sin suna himmatuwa wajen fadada ayyukan da suke yi a kasashen waje, musamman a wadannan shekaru 10, tun bayan da kasar ta bullo da ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a fannin kiwon lafiya, ayyukan likitocin kasar Sin sun fadada daga ceton rayuka da kulawa da marasa lafiya, har zuwa taimakawa kasashe wajen inganta tsarin kiwon lafiya, da karfafa kwarewarsu wajen samar da hidimomin kiwon lafiya. Wato daga samar da agaji, har zuwa inganta hadin-gwiwa mai dorewa, kasar Sin tana kokarin marawa kasashe daban-daban baya, don samun babban ci gaba.

Kasar Sin na kokarin zamanantar da kanta a halin yanzu, kuma a matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, a yayin da take raya kanta, tana kuma tsayawa ga taimakawa zamanantar da sauran kasashe.

LABARAI MASU NASABA

Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO

An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana

Tsawon shekaru 60 ba karshe ne ba, akasin haka, sabon mafari ne. (Murtala Zhang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO
Daga Birnin Sin

Ma’aikatar Cinikayyar Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Shekarar 2025 Game Da Biyayyar Amurka Ga Ka’idojin WTO

October 17, 2025
An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

An Kara Habaka Sabon Karfin Samar Da Kayayyaki Da Hidimomi Mai Dorewa a Cikin Watannin Tara Na Farkon Bana

October 17, 2025
Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki
Daga Birnin Sin

Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki

October 17, 2025
Next Post
Dabarun Gyaran Gashin Kai A Gida

Dabarun Gyaran Gashin Kai A Gida

LABARAI MASU NASABA

Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

Dalilin Bankin AfDB Na Yin Hadaka Da WFP Da IFPRI

October 18, 2025
An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba

An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba

October 18, 2025
Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba

Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba

October 18, 2025
Ƴansanda Sun Kama Gungun Masu Sojan Gona Suna Aikata Laifuka A Kano

Ƴansanda Sun Kama Gungun Masu Sojan Gona Suna Aikata Laifuka A Kano

October 18, 2025
Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna

October 18, 2025
Radda

Gwamnan Katsina Ya Bukaci Al’umma Su Hada Hannu Da Gwamnati Wajen Kawar Da Matsalar Tsaro

October 18, 2025
Yajin Aikin ASUU: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki, Za Ta Gana Da Ministan Ilimi

Yajin Aikin ASUU: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki, Za Ta Gana Da Ministan Ilimi

October 18, 2025
IMF

Fitar Da Kudi Ta Haramtacciyar Hanya Na Kara Dagula Matsalar Tattalin Arziki – IMF

October 18, 2025
majalisar kasa

Majalisar Wakilai Ta Gayyaci CBN Da Bankuna Kan Cire Wa Kwastomomi Kudi Ba Dalili

October 18, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

Matashi Ya Kashe Ɗan Acaɓa Don Neman Kuɗin Auren Mace Ta Uku A Bauchi

October 17, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.