• English
  • Business News
Sunday, October 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Ta Shawarci Kasashen Da Suka Mallaki Makaman Nukiliya Kada Su Yi Amfani Da Shi Wajen Kaiwa Juna Hari 

by Sulaiman and CGTN Hausa
1 year ago
in Daga Birnin Sin
0
Sin Ta Shawarci Kasashen Da Suka Mallaki Makaman Nukiliya Kada Su Yi Amfani Da Shi Wajen Kaiwa Juna Hari 
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa

Sin Ta Yi Kira Ga Kasa Da Kasa Su Ki Amincewa Da Takunkumin Bangare Daya

Shugaban tawagar Sin, kana darektan sashen kayyade jan damara na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sun Xiaobo ya ce, Sin na shawartar kasashe 5 dake mallakar makaman nukiliya, da su sa hannu kan yarjejeniyar hana kaiwa juna hari ta amfani da makaman nukiliya da farko, ko ba da sanarwa mai alaka da hakan, da zummar rage kalubalen tada yake-yake ta amfani da makaman nukiliya a wasu muhimman yankuna. Yana mai cewa Sin ta gabatar da shawararta game da daftarin da abubuwa da za a sanya cikin wannan yarjejeniya.

Sun Xiaobo ya bayyana haka ne jiya, yayin jawabinsa a muhawarar taron share fage karo na biyu na babban taron sauraro da nazarin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya karo na 11 da ake yi a Switzerland.

  • Yahoo: Facebook Ya Kulle Asusun ‘Yan Nijeriya 63,000 
  • Xi Jinping Ya Ba Da Amsar Wasikar Dukkan Ma’aikatan Kamfanin Zirga-zirgar Jiragen Sama Na Xiamen

A cewarsa, Sin na kira ga al’ummun duniya da su aiwatar da matsaya daya da aka cimma game da rage makaman nukiliya, wato kasashe 2 mafiya karfin makaman nukiliya, su sanya sauke nauyin dake bisa wuyansu yadda ya kamata a gaban komai, kuma kada su bi hanyar da ba ta dace ba. Ya ce Sin na kalubalantar Amurka ta yi watsi da shirinta na sayar da makaman nukiliyarta ga kawayenta da ma amfani da makaman wajen ba su kariya, da janye makaman da ta girke a ketare da yin watsi da shirin girke na’urorin kakkabo makamai masu linzami a duniya, da dakatar da girke na’urar kakkabo makamai masu linzami ta LRHW a yankin Asiya da Pacific.

Wakilin na Sin ya kuma jaddada cewa, Sin ta kan tsaya kan matsayin hana yaduwa da murkushe makaman nukiliya a dukkan fannoni a duniya, kuma ta yi alkawarin ba za ta yi amfani da irin wannan makami wajen kai hari da farko ba, kuma ba za ta yi amfani da makaman kan kasashe da yankuna da ba su da makaman nukiliya ba. (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

An Dakatar Da Jami’in Hukumar NIS Saboda Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi

Next Post

Gwamnati Ba Za Ta Yi Amfani Da Karfi Ba Akan Masu Zanga-zanga – Minista

Related

Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa
Daga Birnin Sin

Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa

5 hours ago
Sin Ta Yi Kira Ga Kasa Da Kasa Su Ki Amincewa Da Takunkumin Bangare Daya
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Kasa Da Kasa Su Ki Amincewa Da Takunkumin Bangare Daya

6 hours ago
Kasar Sin Ta Soki Matakan Harajin Amurka “Na Ramuwa” A WTO
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Soki Matakan Harajin Amurka “Na Ramuwa” A WTO

7 hours ago
Jami’in MDD: Shawarar GGI Za Ta Jagoranci Duniya Zuwa Samun Kyakkyawar Makoma Mai Cike Da Adalci
Daga Birnin Sin

Jami’in MDD: Shawarar GGI Za Ta Jagoranci Duniya Zuwa Samun Kyakkyawar Makoma Mai Cike Da Adalci

8 hours ago
Xi Da Takwaransa Na Bangladesh Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kulla Alakar Kasashensu
Daga Birnin Sin

Xi Da Takwaransa Na Bangladesh Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kulla Alakar Kasashensu

10 hours ago
Fim Na Nezha 2 Na Kasar Sin Ya Kara Samun Lambar Yabo
Daga Birnin Sin

Fim Na Nezha 2 Na Kasar Sin Ya Kara Samun Lambar Yabo

1 day ago
Next Post
Gwamnati Ba Za Ta Yi Amfani Da Karfi Ba Akan Masu Zanga-zanga – Minista

Gwamnati Ba Za Ta Yi Amfani Da Karfi Ba Akan Masu Zanga-zanga - Minista

LABARAI MASU NASABA

Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

October 4, 2025
Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa

Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa

October 4, 2025
Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon d’Or

Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon d’Or

October 4, 2025
Jonathan Ya Ƙaryata Batun Danganta Buhari Da Boko Haram

Jonathan Ya Ƙaryata Batun Danganta Buhari Da Boko Haram

October 4, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Kasa Da Kasa Su Ki Amincewa Da Takunkumin Bangare Daya

Sin Ta Yi Kira Ga Kasa Da Kasa Su Ki Amincewa Da Takunkumin Bangare Daya

October 4, 2025
Kasar Sin Ta Soki Matakan Harajin Amurka “Na Ramuwa” A WTO

Kasar Sin Ta Soki Matakan Harajin Amurka “Na Ramuwa” A WTO

October 4, 2025
Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

October 4, 2025
Jami’in MDD: Shawarar GGI Za Ta Jagoranci Duniya Zuwa Samun Kyakkyawar Makoma Mai Cike Da Adalci

Jami’in MDD: Shawarar GGI Za Ta Jagoranci Duniya Zuwa Samun Kyakkyawar Makoma Mai Cike Da Adalci

October 4, 2025
Nijeriya Ta Samu Kwarin Gwiwar Zuwa Kofin Duniya

Nijeriya Ta Samu Kwarin Gwiwar Zuwa Kofin Duniya

October 4, 2025
Bayan Janyewar Sojojin Kamaru, Boko Haram Sun Dawo Kashe-Kashe A Borno

Bayan Janyewar Sojojin Kamaru, Boko Haram Sun Dawo Kashe-Kashe A Borno

October 4, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.