Kamfanin Meta mai Manhajr Facebook a ranar Laraba, ya sanar da cewa ya kulle asusun Facebook kusan 63,000 na ‘yan Nijeriya da ke yunkurin yin zamba a Amurka.
Meta ya ce “‘yan damfarar na kokarin yaudarar Maza ne ta hanyar amfani da suna ko hotunan Mata a Amurka kuma suna amfani da asusun karya don sakaya asalinsu” in ji Meta.
‘Yan damfara ta yanar gizo a Nijeriya, wadanda aka fi sani da ‘Yahoo Boys’, sun yi kaurin suna wajen yin zamba da suka hada da bayyana kansu a matsayin masu bukatar tallafin kudi, Manyan Mutane a Nijeriya, ko masu saka hannun jari ko kuma a siffar masu neman masoya don auratayya da ‘yan kasashen waje, da dai sauransu.
Talla