Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya ce gudanar da baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin na CIIE, wani muhimmin mataki ne ga Sin na fadada bude kofa, kana wani mataki na a aikace na inganta gina tattalin arzikin duniya mai bude kofa. Yana mai cewa, a shirye Sin take ta yi amfani da damar CIIE wajen hada hannu da dukkan bangarori domin fadada bude kofa da bangarorin hadin gwiwa, ta yadda damarmakin dake akwai a kasar Sin za su kasance babbar kasuwa da dukkan kasashen duniya da dubban iyalai za su ci gajiyarta.
Za a bude baje kolin CIIE karo na 7 ne a mako mai zuwa. Yanzu haka, kusan an kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da bikin. Bisa alkaluma, kamfanoni 297 daga cikin manyan kamfanoni ja gaba a duniya guda 500, da kusan rukunoni 800 na masu sayayya daga kasashe da dama, za su shiga a dama da su cikin baje kolin, wanda ya zama wani adadi mafi yawa a tarihi. Baje kolin na bana, zai taimakawa kasashe 37 mafiya karancin tattalin arziki a duniya su shiga cikin shirye shiryen nune-nunen kasa da na kamfanoni, tare da kara fadada yankun baje kolin kayayyakin Afrika a bangarorin nune-nune kayayyakin abinci da na gona, domin ba karin kasashe masu tasowa damar shiga tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya. (Fa’iza Mustapha)