A jiya Asabar ne aka tsayar da tauraron dan Adam mai karbar umarni daga kasa, samfurin Queqiao-2, da rokar Long March-8 Y3, a cibiyar harba kumbuna ta Wenchang, dake lardin Hainan na kudancin kasar Sin, a wani bangare na shirin harba su zuwa samaniya.
A cewar hukumar lura da sararin samaniyar Sin ko CNSA, nan gaba cikin ‘yan kwanaki masu zuwa, a lokaci mafi dacewa za a harba sabon tauraron.
Queqiao-2, ko Magpie Bridge-2, zai rika ba da hidimomi ga zango na 4, na shirin binciken duniyar wata na Sin, da hidimomin sadarwa ga na’urorin binciken Chang’e lamba 4, da 6, da 7, da Chang’e-8. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp