A yau Lahadi ne hukumomin gwamnatin kasar Sin suka ware karin yuan miliyan 350 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 50 don taimakawa yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a biranen Beijing da Tianjin, da lardin Hebei da kuma lardunan arewa maso gabashin kasar Sin.
Ya zuwa yanzu, gwamnatin kasar ta riga ta ware yuan miliyan 520 a cikin asusun ba da agajin bala’o’i na kasar ga wadannan yankunan da bala’in ya shafa, a cewar ma’aikatar kudi da ma’aikatar agajin gaggawa.
Bugu da kari, yau Lahadi, kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta kasar Sin ta ba da labari cewa, bayan aukuwar bala’in ambaliyar ruwa a birnin Zhuozhou na lardin Hebei, kungiyar ta dauki mataki nan da nan ta tattara rukunoninta zuwa wurin da bala’in ta yi kamari, don kaurar da mutane dake fama da bala’in. Ya zuwa karfe 10 na daren jiya, rukunoni 14 masu mambobi fiye da 200 sun kaurar da fararen hula a wurare 1475.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, a ran 1 ga watan nan, kungiyar ta dauki matakin gaggawa mai maki 4, don baiwa wuraren dake fama da bala’in kayayyakin tallafi, ciki har da tantuna da gadaje dake nadewa da kayayyakin magance bala’i da dai sauran kayayyaki 7700, tare da samar da kudade RMB Yuan miliyan 20 wajen tsugunar da mutanen da farfado da zaman rayuwa a yankin Beijing, Tianjin da lardin Hebei. A ran 3 ga watan kuma, kungiyar ta kara samar da kayayyaki 5260 bisa bukatun mutane a Zhuozhou. Bisa shirin da aka tsayar, kungiyar za ta yi kokarin ba da tallafin jin kai ga birnin, ya zuwa yanzu birnin ya samu kayayyakin tallafin da yawansu ya kai fiye da Yuan miliyan 2.5.
Ran 5 ga watan, ana kusa da karshen aikin ceto, kungiyar ta fara aikin kashe kwayoyin cuta a wurin. (Mai fassara: Yahaya, Amina Xu)