Yau Lahadi, kwamitin ci gaba da yin gyare gyare na kasar Sin ya ware kudin RMB yuan miliyan 350 cikin gaggawa don tallafawa farfado da lardunan Henan, Shaanxi da kuma Sichuan wadanda suke fama da bala’in ambaliyar ruwa, musamman ma a fannonin maido da kayayyakin ban ruwa da manyan abeben more rayuwa kamar makarantu da asibitoci, da kuma kayayyakin ba da hidimomi na jama’a, ta yadda za a inganta maido da tsarin rayuwa da aiki yadda ya kamata. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp